Hello and Welcome to UTME CBT FREE Practice Test - Hausa - Set 1

  1. You are to attempt 40 Objectives Questions ONLY for  30 minutes.
  2. Supply Your Full Name in the text box below and begin immediately.
  3. Your time starts NOW!
Full Name (Surname First):

A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.

I
A wani gari can yamma da Magumi, wai shi Tsauni, an yi wani yaro mai suna Salihi. Iyayensa ba masu wadata ba ne, amma sun yi ƙoƙarin ganin ya yi ilmin boko da na Arabiya. Bayan Salihi ya kamala karatun firamare, sai mahaifinsa Tanimu, ya nema masa makarantar gaba da firamare.

Domin an ce ‘‘Ilimi gishirin zaman duniya.’’ Amma kuma samo wa Salihi babbar makarantar Magumi bai yi wa mahaifiyarsa Ɗahira daɗi ba, don ba ta son ɗanta ya yi nesa da ita. Dalili shi ne ɗansu tilo namiji, sauran huɗun kuwa duk mata ne. Bugu da ƙari, tana jin munanan labarai iri-iri da kan faru a irin waɗannan makarantu.

Bayan Salihi ya isa makaranta, sai ya duƙufa kan karatu gadan-gadan. Zuwansa ke da wuya, sai suka ƙulla abota da wani ɗan ajinsu, wai shi Kasa. Kafin ya ankara, sai da abokinsa ya jefa shi cikin wata ƙungiyar asiri.

Da ya farga da halin da ya shiga, sai ya yi ƙoƙarin fita daga cikinta, amma aka nuna masa ai ba a haka. ‘‘ In har ka ce za ka fice, lallai za a kassara ka, ko ma a halaka ka’’ in ji abokinsa.

Ganin halin tsaka-mai-wuya da ya shiga, sai ya tsayar da shawarar ya fallasa ƙungiyar, in ya so komai ta tafasa ta ƙone. Ya je ya shaida wa shugaban makaranta. Nan take ya sanya jami’an tsaro suka kamo dukkan ‘yan ƙungiyar. Kotu ta yanke musu hukunci, sannan aka kai su gidan jarun.

Da ma an ce, ‘‘ Komai nisan jifa ƙasa za ya faɗo.’’

1. Mece ce dangantakar Salihi da Ɗahira ?

A. Wa da ƙanwa.    B. Uba da ‘ya.    C. Miji da mata.    D. Ɗa da Uwa.


2. Wane take ya fi dacewa da wannan labari ?

A. ‘Ilimi gishirin zaman duniya.’
B. ‘Ramin ƙarya ƙurarre ne.’
C. ‘Alheri danƙo ne …’
D. ‘Ba a fafar gora …’


3. Wane ne ya shigar da Salihi cikin ƙungiyar asiri?

A. Dahiru.    B. Monitansu.    C. Kasa.    D. Malaminsu.


4. Ina aka kai su Kasa bayan an yanke musu hukunci ?

A. Tsauni.    B. Yamma da Magumi.    C. Ga shugaban makaranta.    D. Kurkuku.


5. Wane ne tauraron labarin?

A. Mahaifin Salihi.    B. Salihi.    C. Kasa.    D. Mahaifiyar Salihi.
II
Hausawa wasu mutane ne da suka ba abinci muhimmanci a rayuwarsu, domin duk
wata fafitika da gwama numfashi da ba hammata iska, ana yi wa ciki ne. Wato cikin
biyu: ɗaya ya yiwu an ci an ƙoshi, ko kuma ana cikin halin nema ne.

Kullum, da zaran gari ya waye, wasu tun da jijjifi, za a ga sun fita neman abin da za su ci, su da iyalansu, domin a samu rufin asiri. Saboda haka, ba a barin kowa a gida sai tsofaffi da mata da yara da kuma ragwage, kowa ya tafi neman halaliya.

A al’adance, Hausawa suna da lokuta uku na cin abinci a kowace rana, wato safe da rana da dare. A mafi yawan lokuta da safe akan sha abu mai ruwa-ruwa, kamar koko da ƙosai ko kunu. Wasu kuma, sukan ɗumama abin da aka ci a daren da ya gabata. Da rana, kuma akan dafa duk irin abin da ya samu kamar shinkafa da wake ko dambu ko kuma ɗanwake. Da daddare kuma, kusan kowane gida za a sa mu cewa ana dafa tuwo da miya ne, ko miyar kuka ko kuɓewa ko taushe ko kalkashi da dai sauransu, da nama ko babu nama. Duk ko ma mene ne ya samu, wato dai “Daidai ruwa daidai ƙurji.”

Har ila yau, ko da yake ba kowa yake da ƙarfin ɗora girki sau uku ba a rana saboda halin yau, amma a kan sami maƙwabta na gari masu tausayi da lura, su kan kira maƙwabtansu domin su ci abincin, ko suna da shi ko ba su da shi. Da ma tunfil-azal, an san Bahaushe da halin taimako ga ɗan’uwansa.

A zamanin da, za a ga Bahaushe yana ƙoƙarin ya yi noma domin kada gidansa a zauna da yunwa. Amma yanzu, zamananci ya mayar da tunaninsa ya koma kan kasuwanci ko aikin ofis a maimakon aikin gona saboda lalaci da son jiki.

6. Me ake nufi da gwama nunfashi a labarin?

A. Rayuwa.    B. Ka-ce-na-ce.    C. Ƙwazo.    D. Saki-na-dafe.


7. Wane suna ya fi dacewa da wannan labarin?

A. ‘kowa ya daka rawar wani …’
B. ‘Daidai ruwa daidai kurji.’
C. ‘Da ruwan ciki ake jan na rijiya.’
D. ‘Noma tushen arziƙi.’


8. A labarin an nuna baya ga shan abu mai ruwa-ruwa da safe, wasu Hausawa kan

A. yi tuwo    B. dafa shinkafa    C. yi ɗumame    D. turara dambu.


9. A labarin, akan yi ɗan wake da

A. safe    B. rana    C. almuru    D. asuba.


10. Labarin ya na nuna cewa Bahaushe yakan yi noma domin

A. neman kuɗi    B. wadatar zuci    C. ƙarin aure    D. guje wa yunwa.
HARSHE: NAHAWU

11. Wannan alamar (–), ita aka fi sani da

A. waƙafi    B. ruwa biyu    C. karan ɗori    D. ɗebewa.


12. Wanne ne keɓaɓɓen bayanin wasalin /a/?

A. Ɗan gaba ne na sama.
B. Ɗan gaba ne na tsakiya.
C. Ɗan ƙurya ne na sama.
D. Ɗan tsakatsaki ne na ƙasa.


13. Wanne ne ɗan jirge ?

A. /m/.    B. /t/.    C. /l/.    D. /sh/.


14. Wanne ne bare dangane da jinsi?

A. Cinnaka.    B. Hankaka.    C. Buraƙa.    D. Gauraka.


15. A kalmar marubuciya, akwai ɗafi

A. ɗaya B. biyu C. uku D. huɗu.


16. Lokaci Na Yanzu II shi ne mai manunin lokaci

A. –na    B. za    C. –ke    D. -kan.


17. Da ya hango su, ya ce ‘‘Da wa Allah ya haɗa mu?’’

Wannan na nufin da ya hango su, Sai ya

A. gudu B. bi su a guje C. ɓoye D. ja ya tsaya.


Tambayoyi a kan AL’ADU

18. Sanya bante ga yara maza a al’adar Bahaushe, na faruwa ne daga

A. shekara biyu da haihuwa
B. lokacin da yaro ya fara tafiya
C. shekara uku da haihuwa
D. lokacin da aka sha yaro ya warke.


19. Yara masu laƙabi cindo an haife su ne

A. da damina    B. lokacin cin doya    C. da yatsu shida    D. ana ruwa.


20. Ɗan matar da ke aure a gidan da ba a nan ta haife shi ba, shi ne

A. bora    B. mowa    C. agola    D. kado.


21. Barunje shi ne

A. maharbi    B. malami     C. mahauci    D. masaƙi.


22. Makoɗi kayan aiki ne na

A. sassaƙa    B. jima    C. ƙira    D. wanzanci.


23. Wanne ne biki na sana’a?

A. Bikin saukar karatu.
B. Bikin kamun gwauro.
C. Bikin kamun kifi.
D. Bikin kalankuwa.


24. Wace hanya ce ake bi domin shiga harkar bori?

A. Girka.    B. Garaya.    C. Addu’a.    D. Shaushawa.


25. Wace sarauta ce ta shafi kula da baitulmali?

A. Sarkin fada.    B. Ma’aji.    C. Sarkin gida.    D. Waziri.


26. A al’adance, wacce hanya ce aka fi amfani da ita wajen magance ciwo ?

A. Tauna.    B. Turare.    C. Jiƙo.    D. Surace.


27. Me furen tumfafiya kan ƙara wa mutum?

A. Ƙwarinƙashi.    B. Farin jini.    C. Kwarjini.    D. Jarumtaka.


Tambayoyi a kan ADABIN BAKA

28. ‘‘Ja ya faɗo, ja ya ɗauka’’

Wane rukunin adabin baka wannan magana ta fito ?

A. Zuben baka.    B. Maganganun azanci.    C. Salon magana.    D. Waƙoƙin baka.


29. Labarin kura da akuya da harawa yana cikin nau’in labari na

A. tatsuniya    B. kacici-kacici    C. ƙissa    D. almara.


30. ‘‘ƙulun-ƙulu-fita.’’

A. Baba.    B. Gauta.    C. Kanwa    D. Gishiri.


31. Mece ce dangantakar Gizo da Ƙoƙi a tatsuniyoyin Hausa ?

A. Wa da ƙanwa.
B. Ubangida da baranya.
C. Uba da ‘ya.
D. Miji da mata.


32. ‘‘Da duniya da gasƙiya, da

A. ba a bar huntu a kasuwa ba
B. ba a ɗaure ɗan sane ba
C. ba a bar mazari tsirara ba
D. an bar zama da ƙazama.’’


33. Wanne ne gaskiya dangane da makaɗan fada?

A. Ba su yi wa kowa waƙa sai sarki.
B. Ba su karɓar kyauta sai daga sarki.
C. Sarkinsu na sa su yi wa wani waƙa.
D. Dukkansu makaɗan taushi ne.


34. Cikin waɗannan, wanne ne ake kaɗawa?

A. Jauje.    B. Molo.    C. Kwabsa.    D. Garaya.


35. ‘‘Balarabe na Balaraba
Sannu Balaraba
Sai wata rana.’’
Me Haruna Uji, ke nuna wa a wannan
tsakure?

A. Ambaton Balaraba.
B. Dangantakarsa da Balaraba.
C. Ban kwana da duniya.
D. Yabon Balaraba.


RUBUTACCEN ADABI: ZUBE

36. Jigon labarin ‘‘Kowa Ya Daka Rawar Wani’’ na Magana Jari Ce na III na A.
na Imam, ya yi daidai da ‘‘kowa ya

A. Ji a Jikinsa
B. Tsaya Matsayinsa
C. Ji da Kansa
D. Shiga Taitayinsa.’’


37. Labarun cikin Magana Jari ce na III na A. Imam, an shirya su ne bisa salon

A. ji ka ƙaru   B. karɓa – karɓa   C. koyi da kanka   D. zaɓi da kanka.


38. labarin ‘Kowa Ya Dogara Ga Allah, Kada Ya Ji Tsoron Mahassada, Balle
Ƙeta’ na cikin Magana Jari Ce na III na A. Imam, ya amsa sunansa ganin yadda

A. aka halaka Waziri
B. Sarkin Ƙaraya ya cika umarnin Sarkin Sudan
C. aka yi shagalin sarautar Abdun Ugu
D. Abdun Ugu ya ƙetare makircin Waziri.


39. A Ganɗoki na Walin Katsina A. Bello an nuna Ganɗoki ya yi faɗa har da

A. aljannu   B. mata   C. dabbobi   D. sarauniya.


40. ‘Ya zama musu alaƙaƙai, ko wane juyin suka yi na su halaka shi, shi ke sama,
sai ka ce hancin gauta.’ Wane irin salo aka yi amfani da shi a wannan tsakure na Ganɗoki na Walin Katsina A. Bello?

A. Ƙarangiya.
B. Mutuntarwa.
C. Dabbantawa.
D. Kamantawa.

GREAT! You finished before the expiration of the 30 minutes allotted to you. You may want to preview before submission, else, Click the submit button below to see your score

To submit your quiz and see your score/performance report; Make sure you supply your Full Name in the form above.

Unable to submit your quiz? Kindly Click Here To Retake UTME CBT FREE Practice Test - Hausa - Set 1. Make sure you supply your Full Name before submission.Online Learning and Assessment Portal for Nigerian and International Students
error: Content is protected !!