Hello and Welcome to UTME CBT FREE Practice Test - Hausa - Set 2

  1. You are to attempt 40 Objectives Questions ONLY for  30 minutes.
  2. Supply Your Full Name in the text box below and begin immediately.
  3. Your time starts NOW!
Full Name (Surname First):

A karanta waɗannan labaru, sannan a amsa tambayoyin da suka biyo kowannensu.

I
A karkara da ma wasu manyan garuruwa ƙalilan, mutane kan haɗu su riƙa cin abinci tare. Akan zaɓi gidan mutum ɗaya daga cikinsu ya zama shi ne matattara. Mutumin da aka zaɓi gidansa, kusan shi ne shugaba, kuma ya fi kowa yawan shekaru. A wasu lokuta kuma, ana duba gidan da ya fi yalwa, ko ya fi zama kan hanya, babu wahala sosai zuwa gidan, musamman da damina.

A wurin haɗuwa a ci abinci tare, kowane magidanci zai kawo abincin da aka dafa a gidansa, wanda ya fi shiga. Nan fa matan da suka ƙware suke shan yabo da godiya. Waɗanda ba su iya ba kuwa, aiki ya gan su da kuma takaici. Saboda wasu mazan kan yi wa matansu gori. Ba nan ma abin ya tsaya ba, rashin iya abincin nan na iya haddasa mutuwar aure, idan ba a kai hankali nesa ba. Al’amari ya yi muni ke nan.

Cikin abubuwan da ake kawowa, akwai tuwo da shinkafa da fate da ɗan wake da dambu da alkubus da doya da taliya da kuma makaroni. Ana kawo wasu daga cikin waɗannan nau’o’in abinci tare da miya, wasu kuma a siffar dafa-duka. Duka dai wannan, ya danganta da irin cefanen da maigida ya yi.

Akwai alfanu babba game da wannan zama. Da farko, akwai kyautata dangantaka da zaman tare. Ana kuma taimakon juna ta hanyar tattauna matsalolin da suka addabe su. Wanda ma ba ya da ƙarfin yin abinci wani lokaci, ba zai tagayyara ba, zai sami abin da zai ci a wajen.

1. Mutumin da ake haɗuwa, a ci abinci gidansa, yana matsayin

A. wakili B. shugaba C. malami D. hakimi.


2. Mata na kuɓuta daga gorin mazansu saboda iya

A. dafa abinci    B. Magana    C. kyauta    D. cin abinci.


3. A labarin, kalmar ƙware na daidai da

A. haɗu    B. saba    C. dace    D. gwanance.


4. A labarin, nau’o’in abinci nawa aka lissafa?

A. Shida.    B. Bakwai.    C. Takwas.    D. Tara.


5. Babbar fa’idar cin abinci tare, ita ce

A. sada zumunci tsakanin mutane
B. yalwar abinci daban-daban
C. sa mata su ƙara himma
D. wani zai yi santi da abincin wani.
II
‘‘Ba neman aure ke da wuya ba, shigaka-fito’’. Ka ga shiga-ka-fito ɗin nan, lallai shiga-ka-fito ɗin ne! Domin aljihu kan jigata kafin a kai ga biki. Tuddan da al’ada ta tanada, waɗanda dole sai an haye su, suna da yawa.

Yanzu ɗauki misalin kayan na–gani-inaso, wato ’yan kayan nan da ake shiryawa a kai gidan su yarinya a karon farko. Ma’anar yin haka, wai iyaye su san cewa manemin auren ’yarsu da gaske yake. To, ina dole ga yin haka? Da can da yake zuwa yana zance da ’yarsu yana yi mata hasafi, ba a san da gaske yake ba?

Gangaro kan kayan toshi. Nan ma tsabagen kuɗi ake kashewa a sayi suturu da kayan shafe-shafe a kai wa yarinya. Kada fa ka ce zuwa zance da manemi yake yana yi wa yarinya kyauta mako-mako, shi ke nan, ya wadatar.

Ina, ko kaɗan! Kada ka mance da kuɗin gaisuwar iyaye da dukiyar aure kafin a yi baiko da sa ranar biki. Kuɗi ne maɗiɗɗiki ake tanada a kai wa iyayen yarinya da niyyar dai wannan abu da aka ambata.

Duk bayan wannan, ana sa ranar aure, manemin yarinya ya dosa karakaina ke nan daga wannan gida zuwa wancan, ko ma wannan gari zuwa wancan da sunan gayar da iyaye da kakanninta, wai don su san shi.

I, za su san shi mana, tun da ba yana zuwa ne ziƙau ba! Da zarar biki ya kawo jiki kuma, uwa-uba za a shirya kayan lefe na fitar hankali a kai wa yarinya. Nan ma dukiya ake narkawa.

Haƙiƙa duk waɗannan abubuwa al’ada ce kawai ta ƙaƙaba wa al’umma. Ai ta fuskar dukiya, muhimmin abu ga aure, sadaki. Amma abin takaici, yanzu an yi masa mahalli a can ƙarshen sahu!

6. Yaushe manemin yarinya ke zuwa gayar da iyaye da kakanninta?

A. Bayan sa rana. B. Kafin baiko. C. Da soma ganin ta. D. Da an yi biki.


7. Manufar na-gani-ina-so, ita ce bayyana

A. niyya    B. samun duniya    C. asali    D. wurin zama.


8. Shiga-ka-fito wajen neman aure ta fi alaƙa da

A. karakaina    B. gaishe-gaishe    C. kashe kuɗi    D. kamun ƙafa.


9. Ziƙau a labarin na nufin

A. da mummunar kama    B. babu kuɗi    C. babu mutunci    D. a galabaice.


10. Tuddai nawa na neman aure aka ambata?

A. Huɗu.    B. Biyar.    C. Shida.    D. Bakwai.
HARSHE : NAHAWU

11. Alamomin (:) da (-) ana kiran su

A. baka biyu da alamar tambaya
B. saɓi-zarce da aya
C. ruwa biyu da karan ɗori
D. alamar motsin rai da waƙafi.


12. Wace kalma ke da wasula dogaye?

A. Akwati.    B. Ayaba.    C. Tumatir.    D. Kakaki.


13. A lafazin kalma, wane wasali ke ganɗanta |g|?

A. /a/.    B. /u/.    C. /o/.    D. /e/.


14. Wacce ke da hanyar jam’i daban?

A. Kwando.    B. Hula.    C. Rumbu.    D. Ƙwabri.


15. Unguwanni, kalma ce mai gaɓoɓi

A. bakwai    B. shida    C. biyar    D. huɗu.


16. Mene ne mabuɗin jumla?

A. Yankin bayanau.    B. Yankin suna.    C. Yankin aikatau.    D. Yankin karɓau.


17. Idan aka kira mutum inuwar giginya ana nufin ba ya kyautata wa

A. kansa    B. makusantansa    C. magabatansa    D. kowa.


Tambayoyi a kan AL’ADU

18. Akan kira ɗan da aka haifa bayan tagwaye

A. Cindo    B. Audi    C. Gambo    D. Damina.


19. Kwana nawa mace ke yi a lokacin takaba?

A. Ɗari da talatin.    B. Ɗari da arba’in.    C. Ɗari da hamsin.    D. Ɗari da sittin.


20. Wanda shaƙuwar abota ta haɗa ku, shi-ne

A. aboki    B. shaƙiƙi    C. amini    D. masoyi.


21. Wace sana’a ce aka fi sanin mata zalla da yi?

A. Ginin tukwane.    B. Saƙar tabarma.    C. Kaɗi.    D. Ɗinki.


22. Ɗanmaraya Jos ya na amfani ne da

A. kuntigi    B. gurmi    C. garaya    D. molo.


23. Daga cikin waɗannan bukukuwa a wanne ne ake ɗauri?

A. kalankuwa.    B. buɗar dawa.    C. Sallar gani.    D. Sallar idi.


24. Ana danganta itaciyar tsamiya da

A. ’yan ruwa    B. gajimare    C. ƙwanƙwamai    D. dodanni.


25. Daga cikin muhimman ayyukan waziri, akwai

A. saukar da baƙi
B. ɗaukar nauyin baƙi
C. ba wa sarki shawara
D. kula da gidan sarki.


26. Ana fitar da mataccen jini daga jiki ta hanyar

A. rauni    B. ƙaho    C. sakiya    D. tsaga.


27. Wanne ne bare daga cikin magungunan da magori ke bayarwa?

A. Sassaƙe.    B. Turare.    C. Laya.    D. Shafi.


Tambayoyi a kan ADABIN BAKA

28. Yadda ake samun tatsuniya a bakunan tsofaffi, haka ake samun ƙissa a
bakunan malaman

A. fiƙihu    B. tsibbu    C. tarihi    D. hisabi.


29. ‘‘Na haƙa ta ƙi haƙo, na rufe ta ƙi rufo.’’

A. Wata.    B. Rana.    C. Marmara.    D. Inuwa.


30. Wanne ne gaskiya dangane da ƙissa?

A. Yara ake yi wa don koyon tarbiyya.
B. Tana da alaƙa da addini.
C. Dole a samu Gizo da Ƙoƙi a cikinta.
D. Dole a samu aljanu a cikinta.


31. ‘‘Neman magana, an ce da

A. malami, gardi
B. gwauro, yaya iyali?
C. wawa, uwarsa ta mutu
D. ɓarawo ya gudu.’’


32. Wanne ne habaici daga cikin waɗannan?

A. Kano tumbin giwa.
B. Ƙaton kai kamar tulu.
C. Tsame tsakin tsamiya daga tsakin tsada.
D. Da karo-karo giwa ta fi kowa.


33. Su wa suka fi yin waƙoƙin talla?

A. ’Yan yara.    B. ’Yan maza.    C. ’Yan galura.    D. ’Yan mata.


34. Wane rukunin waƙoƙin mata aka fi sani da batsa da zage-zage?

A. Na daka.    B. Na raino.    C. Na talla.    D. Na daɓe.35. A ina yara mata suke waƙe-waƙensu na gaɗa?

A. Gidan amarya.    B. Gidan tsohuwa.    C. Dandali.    D. Zaure.


RUBUTACCEN ADABI: ZUBE

36. Abu na farko cikin ashirin da Waziri
Aku ya faɗa wa ɗansa Fasih, a Magana
Jari Ce Na III, na A. Imam, shi ne

A. dangana ga Allah     B. girmama jama’a     C. lura da mutane     D. taimakon mutane.


37. Wane ne tauraron labarin ‘Kwaɗayi
Mabuɗin Wahala…’ na Magana Jari Ce
Na III na A. Imam ?

A. Ɗandamau.     B. Sarkin Fawa.    C. Sarkin Fada.    D. Nababan – Jaji.


38. Marubucin Shaihu Umar ya yi amfani da salon harshe mai

A. ban haushi    B. kaushi    C. ƙarangiya    D. ban tausayi.


39. Abin da ya mamaye labarin Shaihu Umar shi ne

A. noma da kiwo
B. bauta da cinikin bayi
C. karatu da almajiranci
D. farauta da noman rake.


40. Tsirar da Shaihu Umar ya yi shi kaɗai bayan hadari, ta ba da damar

A. ƙayata labarin
B. taƙaita labarin
C. gintse labarin
D. ci gaban labarin.

GREAT! You finished before the expiration of the 30 minutes allotted to you. You may want to preview before submission, else, Click the submit button below to see your score

To submit your quiz and see your score/performance report; Make sure you supply your Full Name in the form above.

Unable to submit your quiz? Kindly Click Here To Retake UTME CBT FREE Practice Test - Hausa - Set 2. Make sure you supply your Full Name before submission.Online Learning and Assessment Portal for Nigerian and International Students
error: Content is protected !!